Garkuwa da Mutane a Mahuta | |
---|---|
Garkuwa da Mutane | |
Bayanai | |
Ƙasa | Najeriya |
Kwanan wata | Disamba 2020 |
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya |
Jiha | Jihar Katsina |
A watan Disamba na 2020, sama da ɗaliban Islamiyya 80 na makarantar Hizburrahim Islamiyya aka yi garkuwa da su a kan hanyar su ta komawa gida daga wajen wani bikin addini a Jihar Katsina, Najeriya.[1][2][3] Ƴan sakai ne suka kuɓutar da ɗaliban bayan musayar wuta a daji da ƴan ta'adda.[4][5][6][7][8][9][10]
A wani ƙari bayan kuɓutar ɗaliban su 80, ƴan sa kai sun samu nasarar ƙarin kuɓutar da wasu ɗaliban su 33 waɗanda masu garkuwa da mutane suka daɗe da yin garkuwa da su.[11][4]